BBC navigation

Fada na kara muni a kokarin kwace Aleppo

An sabunta: 28 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 19:27 GMT
Mayakan 'yan tawaye a birnin Aleppo na Syria

Mayakan 'yan tawaye a birnin Aleppo na Syria

Fada game da birnin Aleppo na Syria ya kara kazanta, tare da rahotannin wasu munanan artabu da aka gani cikin makonni

Dakarun 'yan tawaye sun kaddamar da wani sabon farmaki a kan sojojin Syria a ranar Alhamis, suna masu cewar yanzu ne aka soma fafatawa domin kwace ikon birnin Aleppon

Amma rahotanni daga birnin na nuni da cewa da kyar 'yan tawayen suka sake samun damar kara kutsa kai cikin birnin.

Masu fafutuka da kuma magidanta a Aleppo sun ce fadan ya kara bazuwa zuwa wasu lardunan da a da ake zaune lafiya, kuma a yanzu ma kungiyar mayakan 'yan awaren Kurdawa ta Turkiyya wato PKK, ta shiga cikin fadan.

Ana zargin dai cewa kungiyar ta Kurdawa 'yan aware na goyon bayan dakarun dake biyayya ne ga shugaba Assad.

Akwai rahotannin gwabza fada a wasu yankunan kasar na Syria, ciki har da Deir -ez-Zor dake gabashin kasa, inda masu fafutuka suka bada labarin cewa an akshe mutane da dama ta hanyar tara su a bindige , ba tare da masu shari'a ba.

Shi dai aikata irin wannan kisa yana neman zama ruwan dare a halin da ake ciki.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.