BBC navigation

Dakarun AU sun 'kame' Kismayo a Somalia - Kenya

An sabunta: 28 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:15 GMT
Dakarun kungiyar Tarayyar Afirka AU

Dakarun kungiyar Tarayyar Afirka AU

Rundunar Sojin kasar Kenya ta ce dakarun kungiyar Tarayyar Afirka AU sun kai farmaki birnin Kismayo, birnin da 'yan tawaye suka mamaye, inda suka karbe ikon wasu bangarori.

Birnin mai tashar jiragen ruwa ya kasance karkashin ikon kungiyar al-Shabab mai alaka da kungiyar al-Qaeda.

Mai magana da yawun kungiyar ta Al-Shabab ya shaidawa kamfanonin dillancin labarai cewa ana ci gaba da gwabza kazamin fada.

Shi kuwa kakakin rundunar sojin kasar Kenyar, Cyrus Oguna ya tabbatarwa da BBC cewa an karbe wasu bangarori na birnin Kismanyo, kuma ana sa ran karbe ragowar cikin dan kankanin lokaci.

Mr Oguna ya ce matakin da rundunar dakarun kasar Kenya da na gwamnatin kasar Somalia suke dauka ya fara ne da tsakar daren jiya Alhamis, sai dai ya ce kawo yanzu ba su iya tantance yawan adadin wadanda suka rasa rayukansu ko jikkkata ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.