BBC navigation

An kori Bo Xilai daga jam'iyya

An sabunta: 28 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 14:46 GMT

Bo Xilai, dan siyasa a China

Kamfanin dillacin labarai na China Xinhua, ya bada rahotan cewar an kori Bo Xilai daga jam'iyyar kwaminisanci ta kasar, zai kuma fuskanci wasu tuhume tuhume.

Kafin ya samu kansa cikin wannan badakalar mai dakinsa ta amince cewar ita ce ta hallaka dan-kasuwar nan na Burtaniya.

Kamfanin dillacin labaru na Xinhuan yace Mr. Bo ya take dokokin da'ar jam'iyyarsa, ya kuma yi amfani da mukaminsa domin amfanin kansa, inda ya karbi cin hanci, da kuma yin huldar da bata dace ba, da mata da dama.

Wannan dai wani mataki ne da zai girgiza jam'iyyar kwaminis mai mulkin kasar ta China.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.