Hajji: an hana jakadan Najeriya ganin maniyyata

Hukumomin Saudiyya sun hana jakadan Najeriya a kasar ganin mata mahajjata 'yan Najeriya da aka tsare a Jeddah bisa hujjar cewa, sun shigar kasar domin yin aikin Hajji ba tare da muharrami ba.

Tuni dai hukumomin Saudiyyar suka dawo da mata mahajjatan 'yan Najeriya fiye da dubu zuwa gida.

Kuma har yanzu hukumomin Saudiyya ba su bada fuska ba ga tagawar da gwamnatin Najeriya ke shirin aikewa kasar domin tattauna wannan batu karkashin jagorancin kakakin majalisar wakilai, Hon. Aminu Waziri Tambuwal.

Jama'ar Najeriyar da dama da sauran malaman addinin Musulunci na ci gaba da tofa albarkacin bakin su dangane da matakinda kasar Saudiyya ta dauka na hana matan gudanar da aikin hajjin na bana.

Yayin da dai wasu ke ganin an ci zarafi da wulakanta 'yan Najeriyar, wasu kuwa cewa su ke wasu 'yan Najeriya na da laifi idan aka duba yadda su ke gudanar da al'amurran da suka sabawa dokokin kasar ta Saudiyya da kuma wasu halaye da akan danganta da 'yan Najeriya a kasar.

Muharrami

Maganar rashin muharrami, wadda ita ce makasudin hana wa wasu mata maniyyata 'yan Najeriya shiga kasar Saudiyya domin su sauke farali, kamar yadda mahukuntan kasar Saudiyyar ke ikirari za a iya cewa har yanzu tana nan jikakka, duk kuwa da tuntubar juna da wadanda abin ya shfa suka ce suna yi.

Mahukunta a Najeriyar dai za a iya cewa suna fuskantar matsin-lamba kwarai da gaske saboda 'yan kasar sun zuba musu ido wajen ganin irin rawar da za su taka wajen ganin cewa an daidaita al'amura an kyale maniyyatan sun yi ibadarsu.

Majalisar dattawan Najeriyar ta zartar da kudirin da ya bukaci shugaban Najeriyar da ya nuna shi ma da gaske yake yi.

Shugaban majalisar, Senata David Mark ya ce: "mun yanke shawarar cewa shugaban kasa ya buga wa Sarkin Saudiyya waya da kansa, ya neme shi da ya taimaka, kasancewar aikin hajji ginshiki ne a tsakanin ginshikan da addinin musulunci ya ginu a kansu. Kuma zai kasance abin takaici idan wadanda ake magana a kansu ba su damar yin ibadarsu ba."

Ita ma majalisar wakilan Najeriyar ta nemi gwamnatin kasar ta gaggauta daukan mataki wajen warware matsalar.

Hasali ma, Kakakin majalisar ne zai jagoranci wani ayari na musammman da zai yi tattaki zuwa kasar Saudiyyar don ganawa da mahukuntan kasar da nufin samun maslaha.

Wa'adi

Sakamakon irin wannan matsin-lambar da gwamnatin Najeriyar ke fuskanta, tun a ranar Laraba ofishin mataimakin shugaban Najeriya ya gana da jekadan kasar Saudiyya da ke Najeriya Khalid Abdu Rabbu, inda ya nuna fushin gwamnatin Najeriya game da tsarewa da tisa keyar wasu mata maniyyatanta zuwa gida, tare da bai wa kasar Saudiyyar wa'adin sa'o'i ashirin da hudu domin a kyale matan su samu damar yin aikin hajji.

Jekadan dai ya tabbatar da cewa za a daidai ta kafin wa'adin ya cika.

Kazalika shi ma kakakin majalisar wakilan ya gana da Jekadan kasar Saudiyya a Najeriya, inda a nan ma ya tabbatar da cewa za a warware matsalar.

Sai dai bayanan da ke fitowa daga ofishin jekadanci na nuna cewa har zuwa maraicen Alhamis babu abin da mahukuntan kasashe biyun ke yi sai tattaunawa.

Dangane da batun wa'adin kwana guda da Najeriyar ta baiwa Saudiyya kuwa, Ofishin jekadancin cewa ya yi ba maganar wa'adi yake yi ba, shi dai ya dukufa ne wajen ganin an warware rigimar da gaggawa.

Laifin wa?

Sai dai wani abu da ke daure kai shi ne yayin da mahukuntan kasar Saudiyyar ke ikirarin cewa nan ba da dadewa ba za a daidaita, kasar saudiyyar ba ta daina tiso keyar mata maniyyyata 'yan Najeriya da ake zargin ba su da muharramai zuwa gida ba.

Wannan takaddama dai ta sa wasu na zargin cewa baya ga maganar muharrami ba za a rasa wani dalilin boye da ya sa kasar Saudiyyar ta tsananta mataki a kan 'yan Najeriyar ba, saboda yayin da Jekadanta a Najeriyar ke cewa maganar muharrami doka ce ta shara'a da ta shafi kowace kasa, rahotanni na cewa 'yan Najeriya ne kadai suka zama saniyar-ware ake tsaurara ta a kansu.

Sai dai a daya hannun, wasu na ganin cewa idan ikirarin mahukuntan Saudiyyar ya tabbata gaskiya, to su ma jami'an da ke gudanar da harkokin aikin hajji a Najeriya na da nasu laifi da ake dangantawa da sakaci wajen cika sharuda, kasancewar da su ake tattaunawa game da aikin hajji a kowace shekara, musamman irin sauye-sauye da za a samu da kuma ka'idoji.