BBC navigation

An maida Omar Khadr wani gidan kurkuku a Canada

An sabunta: 29 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 17:47 GMT
Omar Khadr

Omar Khadr zai kammala zaman gidan yarin sa a Canada

An maida mutumin da yafi kowa karancin shekaru a wurin tsare mutane na Guantanamo zuwa Canada domin ya kammala zaman gidan yarin sa.

Omar Khadr yana da shekaru 15 a lokacin da aka kama shi a fagen yaki a Kasar Afghanistan shekaru 10 da suka gabata.

Ya dai amsa laifinsa a shekarar 2010 na kashe wani sojin Amurka

Omar Khadr ya shafe fiye da kashi daya bisa ukun rayuwar sa a gidan kurkuku

Bayan da ya nemi ai masa afuwa ne, ake rage yawan shekarun da zai yi a gidan yari daga shekaru sama da 40 zuwa shekaru 8

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.