BBC navigation

An tura sojoji su bada kariya a motoci a Honduras

An sabunta: 29 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 06:09 GMT

soji a safa safa a Honduras

Gwamnatin kasar Honduras ta fara tura sojoji su bayar da kariya ga motocin safa dake jigilar fasinja a matsayin wani bangare na yunkurin rage miyagun laifukkan da ake aikatawa a cikin motocin.

Sojoji biyu ne za su rinka zama cikin kowacce motar safa dake sintiri a Teguci-galfa babban birnin kasar da sauran manyan birane.

Shugaba Porfirio Lobo ya ce matakin zai baiwa 'yan sanda damar sintiri a kan titinan kasar.

Gungun masu tafka ayyukan assha suna yawan kai hari a motocin safa-safa dake jigilar fasinja suna kwace wa fasinja da direbobin kudaden su.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.