BBC navigation

Masu kaifin kishin Islama a Mali sun sake rusa hubbaran waliyyai

An sabunta: 29 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 19:14 GMT
Shugaban Mali

Ana ci gaba da rusa hubbarai a Mali

Masu kaifin kishin Islama a arewacin Mali sun sake rusa wani hubbaren waliyyan sufaye.

Mazauna garin Goundam sun ce mutane shakare da wasu motocin daukar kaya ne dauke da gatura da shebur su ka je su ka rushe kabarin da mazauna yankin ke dauka na wani waliyi ne.

Tun a farkon wannan shekara ne dai masu kaifin kishin Islamar su ka kwace iko da arewacin Mali su ka yi ta shan suka, bayan da suka rusa irin wadannan kaburbura da ake cewa na Waliyai ne a birnin Timbuktu.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.