BBC navigation

An sauke mahajjatan Najeriya 529 a birnin Jeddah

An sabunta: 30 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 18:08 GMT
Birnin Jeddan na Saudi Arabia

An dawo da jigilar mahajjata 'yan Najeriya zuwa Saudiyya

Ofishin jakadancin Najeriya a birnin Jeddah na Kasar Saudi Arabia ya tabbatar da cewar an sauke mahajjata 'yan Najeriya su 529 a birnin Jiddan a yau.

Ofishin jakadancin Najeriyar ya ce mata sama da 300 ne a cikin jirgin.

Ofishin ya kara da cewar mahajjatan sun sauka lafiya kuma tuni sun samu damar wucewa ba tare da wata matsala ba

Jakadan Najeriya a birnin Jiddan Ambasada Ahmed Umar ya shaidawa BBC cewar matan da su ka sauka yau, sun isa ne tare da muharraman su.

Dangane da matan da aka komo da su Najeriyar kuwa, jakadan ya ce su na kan tattaunawa yanzu haka tare da hukumomin Kasar Saudiyyan domin ganin an basu damar komowa su sauke faralin su

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.