BBC navigation

Jama'ar Dogon Dawa na neman taimakon tsaro

An sabunta: 18 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:22 GMT
Harin da aka kai garin Dogon Dawa

Harin da aka kai garin Dogon Dawa

Jama'ar garin Dogon Dawa dake karamar hukumar Birnin Gwari ta jahar Kaduna a Najeriya sun bukaci Gwamnati da ta gano wadanda suka kaddamar da hare hare a garin,ta kuma gurfanar da su.

Haka kuma sun bukaci gwamnati da ta dauki matakan hana afkuwar irin wannan ta'asa a gaba.

A wata ganawa da manema labarai da wakilan mutanen wannan gari suka yi da yan jaridu a Kaduna, sun sake jaddada cewar sun mika wa hukumomin yansanda wasikun fargabar da suke da ita kan yiwuwar za a kai musu harin a ranar Lahadin da ta gabata.

Suka ce don haka batun cewar ba su sanar da fargabar ta su ga hukumomi ba, abu ne da ma bai taso ba.

Wakilan al'umar garin sun kuma sake bayyana damuwa a bisa halin rashin tsaron da yankin ya dade a ciki.

Suka ce suna kira ga gwamnati da ta kai masu dauki, saboda yan bindigar dake kai hare hare a yankin sun fi karfinsu.

A ranar lahadin da ta wuce ne dai wasu yan bindiga da ake zargi yan fashi ne suka kai hari a garin suka kuma halaka mutane fiye da ashirin da biyu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.