BBC navigation

Kotu a Masar ta sallami na hannun daman Mubarak

An sabunta: 10 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:31 GMT
Mahara masu zanga zanga kan Rakuma

Mahara masu zanga zanga kan Rakuma

Wata kotu a Kasar Masar ta wanke wani babban jami'i a zamanin Shugaba Mubarak da ake zargi da shirya wani hari da wasu mutane suka kai a kan Rakuma kan masu zanga zangar nuna kin jinin gwamnatin Mubarak din a bara.

Harin wanda shi ne na biyu da aka kai a dandalin Tahrir a watan Fabrairu, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Harin ya kasance daya daga cikin muhimman ababuwan da ake tunawa da shi a lokacin boren da ya hambarar da Shugaba Mubarak daga kan kujerar iko.

Kotun ba ta sami dukkanin mutanen 24 da ake zargi da laifi ba, wadanda suka hada da tsohon kakakin majalisar dokoki da ministoci da kuma 'yan kasuwa.

Wakilin BBC a Kasar yace Misrawa da dama ba za su ji dadin hukuncin ba.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.