BBC navigation

Lebanon: Bam ya kashe mutane 8

An sabunta: 19 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:29 GMT
Harin bam a Beirut

Harin bam a Beirut

An sami fashewar wani babban abu a tsakiyar birnin Beirut na Labanon.

Kamfanin dillancin labarai na Lebanon ya ce, mutane akalla 8 ne suka mutu sannan fiye da 7 suka samu rauni.

Gidan Talabijin na kasar ya nuna hotunan wata karamar motar da ta tarwatse.

Abun ya fashe ne a tsakiyar wata unguwar Ashrafiyeh ta masu hali ta galibin Kiristoci, abunda ya sa motoci da gine gine suka kama da wuta, wani bakin hayaki kuma ya turnike sararin samaniya.

Wadanda suka shedi lamarin sun ce an ji karar fashewar bam din a wasu yankuna masu nisan kilomitoci da yawa.

Lamarin ya faru ne dai yayinda zaman dar dar ke karuwa a Lebanon abinda keda nasaba da rikicin Syria mai makwabtaka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.