BBC navigation

Artabu yayi kamari a zanga zangar Masar

An sabunta: 12 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 19:41 GMT
Masu zanga zanga a dandalin Tahrir na Alkahira

Masu zanga zanga a dandalin Tahrir na Alkahira

Mutane fiye da tamanin ne aka ruwaito cewar sun sami raunuka a artabun da akai a babban birnin Masar na Alkahira tsakanin magoya baya da kuma masu adawa da Shugaba Mursi mai matsakaicin Kishin Islama.

Rahotanni sunce masu zanga zangar sun yi ta jifa duwatsu da ma kwalabai, an kuma cunna wuta a kan manyan motocin bas- bas dake daukar kungiyar 'yan uwa musulmi akalla guda biyu.

A wasu wuraren kuma an kai hari a kan Ofishin Kungiyar yan uwa Musulmin a garin Mahalla a yankin Nile Delta.

Tashin hankalin ya zo ne bayan cece - kucen dake karuwa dangane da wanke wasu tsoffin jami'an gwamnatin Mubarak da wata kotun kasar tayi, bayan an zarge su da bada umarnin kaiwa masu zanga zanga hari a bara.

Wakilin BBC ya ce, bayan kwanaki 100n da Shugaba Mursi yai akan mulki, wannan ita ce zanga zanga mafi girma da ka gudanar a cikin kasar.

Misrawa na cike da fushin cewar, har yanzu Shugaban bai yi wani katabus ba, wajen bunkasa tattalin arzikinsu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.