BBC navigation

'Yan Mau Mau da suka dandani azaba za su iya neman hakkinsu daga Birtaniya

An sabunta: 5 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:07 GMT
Yan Mau Mau na Kenya dake neman diyya

Yan Mau Mau na Kenya dake neman diyya

Babbar Kotu a nan London ta yanke hukuncin cewar Yan Kenya 3n da aka gana wa akuba a zamanin mulkin mallakar Birtaniya a shekarun 1950 za su iya ci gaba da kararsu ta neman diyya daga Gwamnatin Birtaniya.

Alkalin, Mai shara'a McCombe, ya yanke hukuncin cewar akwai wadatacciyar shedar takardu saboda sojin Birtaniya nada sunan ajiye bayanai.

Zaman kotun bai wuce na tsawon minti biyar ba, Alkalin ya yanke hukuncin cewa duk da kasancewar an azabtar da mutanen ne a Kenya kimanin shekaru sittin da suka wuce, akwai yuwuwar a kwatanta masu adalci a shari'ar.

Martin Day na daya daga cikin lauyoyin da suka wakilci yan Kenyar wadanda aka tsare a lokacin boren na Mau Mau, ya kuma ce hukunci ne mai cike da tarihi.

Ya ce "a Kenya akwai sauran dubban mutane wadanda ke raye wadanda kuma su ma aka ganawa irin wannan azaba, da kuma cin zarafi, kwatankwacin irin yadda aka gallaza ma mutane ukun da muke karewa."

Jin sakamakon hukuncin ya janyo kade kade da raye raye har ma da guda, a tsakanin tsoffin mayakan na Mau Mau a Nairobi, babban birnin Kenya.

Wasu mutane a Kenya dai sunce hukuncin ya nuna cewa za a iya gani karara cewar an kwatanta adalci, ko da kuwa bayan shekaru hamsin ne da aukuwar lamari, ni kam na yi matukar farin ciki, domin a yanzu za a yi wa mutanen adalci.

Duk da kasancewa gwamnatin Birtaniya ta ce amsa cewar an azabtar da wadanda aka tsare a lokacin yakin kwatar yancin na Kenya, amma dai ta ce za ta daukaka kara.

A wata sanarwa da ofishin harkokin wajen kasar ya fitar na nuna cewa muhimman wadanda suka kasance masu fada aji a lokacin dokar ta bacin ta Kenya, basa raye a yanzu, don haka ba za su iya bada na su bahasin kan abubuwan da ska faru ba.

Lauyan mutanen dai ya ce za a dauki tsawon kimanin shekara guda kafin a iya warware wannan batu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.