BBC navigation

An sace wasu ma'aikatan agaji 6 a Nijar

An sabunta: 16 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:20 GMT
Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar

Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar

Kungiyoyin bayar da agaji kan harkokin lafiya na BEFEN ta Nijar da kuma ta Alerte Sante ta kasar Chadi sun yi kira ga yan bindigar da suka sace masu ma'aikata da su sako su ba tare da bata lokaci ba.

Kungiyoyin sun yi wannan kira a wajen wani taron manema labari da suka kira a Yamai babban Birnin Nijar.
Suka ce ya kamata yan bindigar su saki mutanen ganin cewa daya daga cikinsu ya samu mummunan rauni a lokacin da yan bindigar suke kokarin sace su.

Ma'aikatan Kungiyoyin 6 ne dai aka sace a daren ranar lahadi a Dakoro.

Bayanan baya bayan nan dai na nuni da cewar yan fashi da mutanen da suke garkuwa da mutanen na cikin kasar ta Nijar a yankin Cintabaraden da ke cikin jihar Tawa, inda jami'an tsaro suka yi masu kawanya.

Wanann dai shi ne lamarin satar mutane na baya baya a kasar ta Nijar bayan da a kusan fiye da shekara gudar ta wuce wasu da ake zargin yan kungiyar Al-Qa'ida a yankin arewacin Afrika -AQIM suka sace wasu Faransawa ma'akatan kamfanin hakar ma'adinin Uranium na Areva a Arlit dake arewacin kasar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.