BBC navigation

Asubitoci na fama da rashin jini a Damagaram ta Nijar

An sabunta: 12 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:19 GMT
Asubiti a Nijar

Asubiti a Nijar

Matsalar rashin jini a asibitoci da wuraren haihuwa na cimma al'umma tuwo a kwarya a Jamhuriyar Nijar .

Hakan ya sa Jami'an dake kula da Bankin jinin asibitin kasa dake Damagaram na shelar neman agaji ta kafofin yada labarai a garin.

Wasu mutanen kuma na amsa wannan kira, inda sukan je domin bayar da kyautar jinin.

Haka kuma wasu kan je da marassa lafiyarsu don samun bashin jinin kafin wasu nasu su je su taimaka.

A duk shekara dai asubitin na kasa na amfani da jikka dubu 4 ta Jini amma tuni a bana har sun yi amfani da jikka dubu 6.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.