BBC navigation

Mutanen da ake safararsu zuwa Birtaniya na kara yawa

An sabunta: 18 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:39 GMT
Fastocin yaki da safarar mutane

Fastocin yaki da safarar mutane

Kamar yadda wani sabon rahoto ya ce, yawan mutanen da ake safararsu zuwa nan Birtaniya daga bisani kuma a rinka amfani da su a matsayin abin lalata da kwadago da kuma bautar cikin gidaje na karuwa.

Nazarin -- wanda ma'aikatun gwamnati da yawa suka yi -- ya ce gungun kungiyoyin masu aikata laifuka na da hannu a haramtacciyar sana'ar.

Galibin wadanda abun ke shafa dai na fitowa ne daga China da Najeriya da kuma gabacin Turai.

A bara sun gano wadanda abun ka iya shafa 946 idan aka kwatanta da 712 a shekara ta dubu 2 da 10.

Sashen Hukumar yansandan Birtaniya da ke da alhakin kai wannan samame ya ce ya kan kai samame sau biyu a kowanne mako a gidajen da ake zargi ana tsare da wadanda ke fuskantar wannan matsala.

Hakan kuma alama ce da ke nuna cewa jami'an tsaron Birtaniya na kokarin shawo kan matsalar da take wahalar tare da musgunawa jama'a.

Sabon rahoton ya nuna cewa matsalar na kara kazancewa, kuma gungun masu aikata laifi daga China da Najeriya, da Vietnam, da Slovakia da kuma Romania sun fi yin barazana ga kasar ta Burtaniya.

Wata kungiya da ke yaki da bauta ta zargi gwamnatin Burtaniya da rashin maida hankali wajen magance matsalar.

A cewar kungiyar har yanzu Burtaniya na kallon matsalar a matsayin wata harka ce da ta shafar shige da ficen baki maimakon ta ci da gumin wasu.

Wata kungiyar ta ce alkalumman da aka fitar dangane da matsalar somin tabi ne.

Ka na rahoton ya bayyana cewa a baya bayan nan Birtaniya ta fuskanci matsalar masu farautar sassan jikin dan adam, inda aka bankado wani shiri na saida kodar daya daga cikin mutanne da aka yi safararsu.

Sai dai minista mai kula da sashen shige da fice na Birtaniya ya ce matsalar ta na bukatar duka sassan gwamnati da hukumomi su shiga cikin lamarin, ka na al'umma su hankalta.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.