BBC navigation

Rwanda da Uganda sun yi watsi da zargin tallafawa yan tawayen Congo

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:00 GMT
Sojin kungiyar 'yantawayen M23 a Congo

Sojin kungiyar 'yantawayen M23 a Congo

Rwanda da Uganda sun dage wajen musanta zargin da wani rahoton majalisar dinkin duniya yayi cewa, suna cigaba da tallafawa 'yan tawayen dake gabashin jamhuriyar Dimukradiyyar Congo.

Ministan hulda da kasashen wajen Uganda, Henry Okello Oryem ya fadawa BBC cewa, majalisar dinkin duniyar na kokari ne kawai ta dorawa wasu alhakin gazawar rundunar samar da zaman lafiyar da ta tura zuwa Congo.

Rahoton dai ya ce Rwanda na ci gaba da goyon bayan yan tawayen Jamhuriyar Demokuradiyar Congo ne ta yadda har abun ya kai Ministan tsaronta James Kabarebe, kusan shi ke jagorantar boren.

Ya ce Uganda ma na goyon bayan kungiyar yan tawaye ta M23, wadda take artabu tare da sojin Congo tun cikin watan Afrilu.

Ba a dai bayyana rahoton a fili ba, to amma an kwarmata shi ga kamfanin dillacin labarai na Reuters.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.