BBC navigation

Sudan ta zargi Isra'ila da kai hari a masana'antar makamanta

An sabunta: 24 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:55 GMT
Masana'antar Makamai ta Yarmouk a Sudan

Masana'antar Makamai ta Yarmouk a Sudan

Gwamnatin Sudan ta zargi Isra'ila da jefa bam a wata masana'antar kera makamai a Khartoum babban birnin kasar ta Sudan wadda gobara ta lashe daren ranar talata.

Ministan watsa labarai Ahmed Bilal Osman ya ce jiragen sama 4 ne suka kai harin a masana'antar Yarmouk.

Ya ce, mutane biyu ne aka kashe.Mazauna yankin sun bayar da rahoton ganin jiragen sama ko kuma makamai masu linzami kafin wasu ababuwa masu yawa su yi farfashewa a masana'antar.

Jami'an Isra'ila sun ki suce uffan.

Sudan ta zargi Isra'ila da kai hare hare da yawa a a cikin yankin kasarta a cikin shekaru hudu da suka wuce.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.