BBC navigation

Marikana: an soma bincike akan kisan ma'aikata

An sabunta: 1 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:01 GMT

maaikan hako maadanai a Afrika ta kudu

Hukumar bincike da gwamnatin Afurka ta kudu ta kafa ta soma zaman ta a yau domin yin bincike akan kisan ma'aikatan hakar ma'adinai talatin da hudu yayin wata tarzoma da aka yi cikin watan Agusta da ya gabata.

Wani alkali mai ritaya ne dai ke jagorantar hukumar binciken da gwamnatin Afurka ta kudu ta kafa akan wannan batu, kuma hkumar binciken na yin zamanta ne a Rustenburg wanda wuri ne dake kusa da inda aka aikata kisan.

Hukumar binciken dai ta bude zaman na ta ne da karanto sunayen wadanda aka kashe a lamarin sannan aka yi tsit na minti guda domin giramama su.

Sannan kuma sai hukumar binciken ta yi watsi da bukatar wasu iyalan wadanda aka kashe dake neman a dage zaman bincike na hukumar.

Hukumar tace, ba za ta jinkirta aikinta ba domin tana bukatar kammala aikinta cikin gaggawa.

Binciken dai zata duba irin rawar da 'yan sanda suka taka, da kuma irin rawar da hukumar kamfanin hakar ma'adinan ta taka.

Hukumar binciken kuma zata duba abinda kungiyoyin kwadago dake hamayya da juna har ya zuwa lokacin da aka aikata kisan.

Kisan dai na Marikana ya aza ayar tambaya ba wai kawai akan yin amfani da karfi da ya wuce kima da 'yan sanda suka yi ba, binciken zai ya tado da batun adalci tsakanin al'ummar Afurka ta kudu da ma irin salon mulkin shugaba Jocob Zuma.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.