BBC navigation

Hajji: an mayar da maniyyatan Najeriya 44

An sabunta: 1 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:34 GMT

Hukumomin Saudiyya sun mayar da wasu maniyyata hajjin bana mata 'yan Najeriya su arba'in da hudu zuwa kasar bisa dalilin rashin kasancewa tare da muharrami.

Maniyyatan da lamarin ya shafa dai sun fito ne daga jihohin Kaduna da kuma Kebbi, kuma sun bar Najeriya ne a jiya.

Maniyyan mata dai sun hada ne da goma sha tara daga jihar Kaduna da kuma ashirin da biyar daga jihar Kebbi

Wannan dai na faruwa ne yayin da ake kokarin warware wannan matsala da ta sa hukumomin Saudiyya su mayar da mata maniyya fiye da dubu zuwa Najeriya.

Yanzu haka dai ana cigaba da tattaunawa akan wannan batu tsakanin jami'an Najeriya da na Saudiyya.

Tuni dai a baya hukumomin Najeriya suka bada sanarwar cewa, sun dakatar da jigilar maniyya zuwa kasa mai tsarki dangane da wannan batu.

Ofishin jakadancin Najeriya a birnin Jeddah yace, ya mika kuka akan wannan batu ga hukumomin Saudiyya

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.