BBC navigation

Syria ta zargi Amurka da taimakon 'yan ta'adda

An sabunta: 1 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 21:05 GMT

Ministan harkokin wajen Syria, Walid al-Moualem, ya zargi Amurka da wasu kashe hudu da ingizawa tare da goyan bayan ta'addanci a kasarsa.

Ya ce Amurka da Faransa da Qatar da Saudiyya da kuma Turkiyya na samar da makamai da kudi ga 'yan tawayen dake fada domin kifar da Shugaba Bashar al-Assad.

Ministan ya fadi hakan ne a jawabin da ya yi a babban zauren taron Majalisar Dinkin Duniya a New York.

Ya gayawa majalisar cewa gwamnatin Syriar ta yi gyare-gyare a harkokin siyasa, ta kuma bayar da hadin kai a tsare-tsaren da wakilan majalisar suka fitar don kawo karshen rikici a kasar.

Ya kuma yi kira ga kungiyoyi na ciki da wajen Syrian da su shiga cikin tattaunawar samar da zaman lafiya.

To amma ya roki kasashen da ya zarga da laifin ingiza 'yan tawaye da su daina.

Yace: "Duk wata nasarar da kokarin kasashen duniya ke iya samu, tare da sadaukar da kan da gwamnatin Syria keyi, na bukatar a tsaida kasashen dake tallafama kungiyoyin dake dauke da makamai a kasata, wadanda Turkiyya da Saudiyya da Qatar da Libya da dai sauransu ke jagoranta, su daina bayar da makamai, da horo da kuma daukar bakuncin kungiyoyin 'yan ta'adda -- su kuma karfafa batun tattaunawa da yin watsi da tashin hankali".

Haka kuma yace kiran da wasu keyi na cewa Shugaba Assad ya sauka daga mulki, tsoma baki ne a harkokin cikin gidan Syrian.

Tun da farko dai babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar, Ban ki-Moon, ya soki gwamnatin Syriar akan kashe-kashen da ake yi a kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.