BBC navigation

Shugaban Venezuela Chavez zai kara da Capriles

An sabunta: 1 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:55 GMT

Shavez da Capriles

Mutane sama da dubu dari ne suka yi taron gangami a babban birnin Venezuela, Caracas don nuna goyon bayansu ga Henrique Capriles wanda za su kara da Shugaban kasar Hugo Chavez a zaben da za a yi mako mai zuwa.

Mr Capriles dai ya soki Mr Chavez kan abin da ya kira rashin cika alkawarurruka a shekaru goma sha hudu da yayi a kan karagar mulki.

Duka bangarorin biyu dai sun yi gangami, amma dai yakin neman zabe na cike da rikici inda aka kashe wasu masu marawa 'yan adawar baya su uku.

Shugaban kasar venezuela Hugo Chavez ya ce ba zai yiwu ya fadi zabe ba. kuma yayi alkawarin zai ci gaba da irin mulkinsa na gurguzu.

Henrique Capriles wanda zai kara da shugaban kasar shavez yayi nasa gangamin a babban birnin Venezuela, Caracas.

Capriles ya yi alkawarin cewa rikici zai gushe kuma shi zai yi nasara a zaben shugaban kasar da za ayi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.