BBC navigation

Shugaban Colombia na da Kansar mafitsara

An sabunta: 2 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 05:13 GMT

Shugaban kasar Colombia, Juan Manual Santos

Shugaban kasar Colombia Juan Manual Santos ya ba da sanarwar cewa yana da cutar Kansar mafitsara; za a kuma yi masa aikin tiyata a ranar laraba.

Mr Santos mai shekaru sittin da daya a duniya ya ce Kansar karama ce an kuma gano ta da wuri.

Yace likitoci sun yi hasashe za a samu nasara casa'in da bakwai bisa dari na cire ta.

Sanarwar ta zo ne mako guda gabanin shirin da aka yi na tattaunawar sulhu da 'yan tawaye masu ra'ayin kawo sauyi na kungiyar FARC da nufin kawo karshen tashin hankalin da aka shafe kimanin shekaru hamsin ana yi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.