BBC navigation

Shugaba Saakashvili ya amsa shan kaye a zaben Georgia

An sabunta: 2 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 19:01 GMT
murnar zaben a Georgia

murnar zaben a Georgia

Shugaba Mikheil Saakashvili na Georgia ya amince cewar jam'iyyarsa ta sha kaye a zaben majalisar dokokin kasar da aka yi.

Mr Saakashvili ya ce a bayyane take bangaren 'yan adawa da aaake yi wa lakabi da Mafarkin Georgia ko kuma Georgian Dream a turance, a karkashin jagorancin Bidzina Ivanishivili, mutumin da ya fi kowa arziki a kasar, na da rinjayen kujeru dari da hamsin a majalisar dokokin.

Wannan shi ne karon farko a tarihin Georgia tun bayan zamanin Tarayyar Soviet da iko zai sauya hannu ba tare da juyin juya hali ba.

Mikheil Saakashvili, wanda ya jagoranci kasar tun 2003 zai ci gaba da zama shugaba har sai wa'adinsa ya kare a badi.

Mr Ivanishvili ya ce yana fatan zama praminista, kuma da zarar hakan ya faru, zai karfafa hulda da kasar Rasha, ya kuma nemi shigar da kasar cikin kungiyar tsaro ta NATO.

Tuni Amurka ta fitar da sanarwa tana yaba wa shugaba Saakashvili kan ayadda ya amince da shan kaye a zaben.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.