BBC navigation

Mutane 36 sun mutu a hadarin jirgi a Hong Kong

An sabunta: 2 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 05:02 GMT

Jirgin Hong Kong

Wani karo da aka yi tsakanin wasu jiragen ruwa na fasinja a gabar ruwan Hong Kong ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane talatin da shida da kuma wasu masu dimbin yawa da suka jikkata.

A yanzu haka dai, ana cigaba da aikin ceto.

Daya daga cikin jiragen ruwan wanda aka dauka haya don ayi shagali yana dauke ne da mutane sama da dari da ashirin.

Jirgin da aka dauko hayar; wanda ya yi taho mu gama da wani jirgin ruwa na fasinja ya nutse dab da tsibirin Lamma.

Bayan aukuwar hadarin nan take mutane 28 suka mutu, yayin da wasu 100 kuma suka jikkata.

An dai garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti, amma wasu takwas daga cikinsu sun mutu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.