BBC navigation

Dakarun Tarayyar Afrika sun shiga Kismayo

An sabunta: 2 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 09:34 GMT
Birnin Kismayo

Birnin Kismayo

Tawagar dakarun kungiyar tarayyar Afrika da na gwamnatin Somaliya sun shiga birnin Kismayo mai tashar jiragen ruwa, kamar yadda jami'ai da shaidu suka bayyana.

Dakarun dai na fafatawa ne da kungiyar masu gwagwarmaya ta Alshabab wajen iko da birnin.

A ranar Asabar din da ta gabata ne Alshabab ta ce ta janye daga Kismayo, bayan wani hari da dakarun tarayyar Afrika suka kai.

Sojojin Kenya da na Somalia ne suka kai harin a kan kungiyar, ta amfani da bakin ruwa a waje na karshe da kungiyar take da karfi, kodayake sun dan fuskanci turjiya.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi wa dakarun kungiyar tarayyar Afrikan gamin-gambiza ne.

Wani mazaunin Kismayo ya shaidawa BBC cewa, sojoji 11 sun shiga Kismayo ta yammacin birnin, kuma suna sintiri da kafa a manyan titunan birnin.

Yayin da wani kuma yace ya ga sojojin Kenya da na Somalia sun shiga Kismayo ta filin jiragen sama dake tsakiyar birnin.

Haka kuma wani dattijo ya ce ya ga dakaru kusan 100 sun karbe caji ofis din 'yan sanda, kuma sun kafa gurare a saman dogayen gine-gine.

Mai magana da yawun gwamnatin Somalia, Mohamed Faarah Daher ya shaidawa BBC cewa, dakarun kungiyar tarayyar Afrika da na Somalia sun shiga Kismayo ne domin samar da tsaro ga mazauna birnin.

Haka kuma sun karbe iko da filin jiragen sama da na jiragen ruwan birnin.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.