BBC navigation

Solskjaer na neman zama manajan Blackburn

An sabunta: 2 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:45 GMT
Tsohon dan wasan Man U, Ole Gunnar Solskjaer

Tsohon dan wasan Man U, Ole Gunnar Solskjaer

Sunan tsohon dan wasan gaba na kulab din Manchester United, Ole gunnar Solskjaer ya shammaci jama'a kasancewarsa daya daga cikin na gaba-gaba a tsakanin masu neman maye gurbin manajan kulab din Blackburn, Steve Kean.

Wakilan Solskjaer, dan shekara 39 da haihuwa, da kuma Tim Sherwood da tsohon manajan kulab din Real Madrid, Bernd Schuster sun nuna sha'awar mukamin.

Solskjaer ya samu nasarar cin gasar League ta kasar Norway a shekararsa ta farko da karbar ragamar Kulab din Molde, kuma kwangilarsa da kulab din za ta kare a shekara ta 2014.

Kuma Manajan kulab din manchester United, Sir Alex Ferguson ya taba yi wa Solskjaer albishir lokacin da ya sanya hannu a kwantaraginsa da kulab din Molde yana cewa "

Inda ya kara da cewa "Idan ka kama aiki da kulab din da bai taba cin league a kasar Norway ba kuma ka ci nasarar cin league, to akwai labari tattare da kai."

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.