BBC navigation

Lennon ya yaba da rawar da Celtic ta taka

An sabunta: 3 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 09:08 GMT
'Yan wasa sun daga Neil Lennon

'Yan wasan Celtic sun daga manaja Neil Lennon

Manajan kulob din Celtic Neil Lennon ya ce "Watakila ni ne mutumin da ya fi kowa alfahari a nahyar Turai" bayan kulob din ya doke Spartak ta Moscow da ci uku da biyu a gasar Champions league.

"Na rasa kalaman da suka dace da zan bayyana rawar da 'yan wasan suka taka, lallai sun nuna kwarewa. "Ya fada cikin farin ciki.

Inda ya kara da cewa "Mutane sun raina kurar Celtic. Domin ba sa mutunta kulob din kamar yadda ya kamata, amma ina ganin rawar da kulob din ya taka zai sauya tunanin wasu."

Nasarar da Celtic ta samu ya sanya ta zama ta biyu a rukunin G, inda take da maki hudu.

Kuma a wasanninsu na gama Celtic za ta kara ne da Barcelona, wanda shi ne karawa na farko a filin wasa na Camp Nou a ranar 23 ga watan Octobar da muke ciki.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.