BBC navigation

An kashe sojojin Najeriya hudu a Darfur

An sabunta: 3 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:26 GMT
Dakarun rundunar UNAMID

Dakarun rundunar UNAMID

An kashe dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka su hudu yayin da takwas suka jikkata a wani kwanton bauna da aka yi musu a yankin Darfur da ke yammacin Sudan.

Rundunar hadin gwiwa ta kiyaye zaman lafiya, wato UNAMID, ta ce an kai hari a kan sojojin hudu 'yan Najeriya ne kilomita biyu daga hedkwatarsu a garin El Geneina.

Wani kakakin rundunar ya ce daga bangarori da dama aka bude wuta a kan ayarin motocin da dakarun ke ciki.

Yanzu haka akwai dakarun rundunar ta UNAMID fiye da dubu goma sha shida wadanda aka dorawa alhakin bayar da kariya ga fararen hula a Darfur tun shekarar 2007.

A cewar UNAMID, an yiwa dakarun nata kwanton bauna ne ranar Talata da dare; ta kuma yi kira ga gwamnatin Sudan ta hukunta 'yan bindigar da suka kai harin.

Tun bayan fara aikinta shekaru biyar da suka wuce, an kashe wa rundunar sojoji saba'in da takwas a Darfur.

Tashe-tashen hankula

Tashe-tashen hankula dai sun ragu a Darfur tun bayan barkewar yakin basasa a shekarar 2003, amma har yanzu a kan samu fito-na-fito tsakanin dakarun gwamnati, da 'yan tawaye, da kungiyoyin kabilun da ba sa ga-maciji da juna.

Sai dai kuma tun bayan ballewar Sudan ta Kudu bara tashe-tashen hankulan sun karu.

'Yan fashi da makami ma na amfani da rashin tsaron da ake fama da shi suna cin karensu babu babbaka a yammacin yankin na Darfur.

Ko a watan jiya an bayar da rahoton mutuwar mutane da dama bayan dakarun Sudan sun gwabza da 'yan tawayen Darfur.

Gwamnatin Sudan na zargin kungiyoyin 'yan tawaye daban daban a Sudan ta Kudu da tallafa wa 'yan tawayen Darfur.

Bara Shugaba Omar al-Bashir ya rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da wadansu kananan kungiyoyin 'yan tawaye, amma dai manyan kungiyoyin sun ki shiga cikin shirin.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.