BBC navigation

An sanya dokar hana fita a Mubi

An sabunta: 3 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 04:33 GMT

Kwalejin da aka kai wa dalibanta hari a Mubi

Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa da ke Najeriya ta ce an sanya dokar hana fita - daga karfe uku na rana zuwa shida na safe - a garin Mubi bayan harin da wadansu mutane da ba a kai ga sanin ko su wanene ba suka kai wuraren kwanan dalibai, lamarin da ya yi sanadiyar rasuwar akalla mutane 25.

Kakakin rundunar, DSP Muhammad Ibrahim, ya shaidawa BBC cewa an fara gudanar da bincike gadan-gaban don gano wadanda suka kai harin na ranar Litinin.

Ya ce:''An zuba jami'an tsaro masu yawa suna patrol (sintiri) a garin Mubi domin gudun sake aukuwar abubuwan da suka faru. Akwai jami'an tsaro masu yawa; akwai jami'an tsaro na farin kaya wadanda ke zagawa cikin gari ko Allah zai sa a kama mutanen da suka kai wadannan hare-hare.''

Wani mazaunin garin ya shaidawa BBC cewa maharan sun bi daki zuwa daki ne suna harbi ko kuma dabawa wadanda abin ya shafa wuka.

Hukumomin 'yan sanda sun ce 'yan bindigar sun kira sunan wasu mutanen, kuma suka kashe su a lokacin da suka bayyana kansu.

Kungiyar dalibai ta kasa a Najeriya ta yi Alla-wadai da wadannan hare-hare.

Wasu na zargin 'yan kungiyar Boko Haram da kai wannan harin, a yayin da wasu kuma ke danganta lamarin da siyasar daliban kwalejin Kimiya da Fasaha ta garin Mubi.

A makon da ya gabata ne jami'an tsaron Najeriya suka kai samame akan wadanda ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne a Mubi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.