BBC navigation

An tafka muhawara tsakanin Obama da Romney

An sabunta: 16 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 12:17 GMT

Obama da Romney

Shugaban Amurka Barack Obama da dan takarar jam'iyyar Republican Mitt Romney sun gudanar da muhawararsu ta farko a kan tattalin arziki kasar.

'Yan takarar sun tafka muhawarar ce a jihar Colorado.

Mista Romney ya yi ta caccakar gwamnatin shugaba Obama game da gagarumin gibin kasafin kudin kasar da kuma matsalar rashin ayyukan yi.

Shi kuwa Mista Obama ya kare kansa inda ya zargi abokin hamayyarsa da yunkurin kirkiro da shirin rage haraji mai yawa ga masu hannu da shuni, da kuma kashe kudi babu gaira babu dalili a kan ayyukan soji.

Akasarin masu sharhi a Amurka sun ce Mista Romney ne ya yi nasara a muhawarar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.