BBC navigation

Dabbobin ruwa sun shige gidajen mutane a Najeriya

An sabunta: 4 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:31 GMT
Ambaliyar ruwa ta mamaye wadansu sassan Najeriya

Ambaliyar ruwa ta mamaye wadansu sassan Najeriya

Wadansu dabbobin ruwa masu hadari ga bil-Adama irinsu kadoji, da macizai, da dorinar ruwa sun gaje gidajen dimbin mutane wadanda ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a Jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya.

Wuraren da ambaliyar ruwan ta 'yan kwanakin da suka gabata ta fi muni a jihar ta Benue su ne Makurdi, babban binrin jihar, da kuma garuruwan Agatu, da Logo, da Otukpo, da kuma Adoka.

Wuese Jirake ya shaida wa BBC cewa lokacin da ya je gidansa domin ganin yanayin da yake ciki, ya tarar da dorinar ruwa:

"A gidana [yanzu haka] akwai dorinar ruwa.... Mun kai rahoto ga gwamnati saboda ba wanda ya turo [dorinar]", inji Mista Jirake.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya, wato NEMA, ta tabbatar da kasancewar muggan dabbobin ruwan a gidajen da ambaliyar ta mamaye.

Babban jami'in tsare-tsare na hukumar a yankin arewa ta tsakiyar Najeriya, Abdussalam Muhammad, ya ce suna hada gwiwa da gwamnatin jihar Benue domin daukar matakin da ya dace don ganin mutanen sun koma gidajensu.

Akwai hadari

A cewar Malam Abdussalam, "Maganar nan da muke yi akwai kadoji da macizai da ma wasu dabbobi wadanda ruwa ya taho da su; to ka ga idan mutane mutane suka nemi su tare a wurin [dabbobin za su] iya yi musu illa".

Jami'in na hukumar NEMA ya kuma bayyana cewa hukumomin Jamhuriyar Kamaru sun bayyana aniyar sake sako ruwa daga madatsar ruwan nan ta Lagdo wadda kan jawo ambaliya a wadansu jihohin Najeriya, ciki har da jihar ta Benue.

Sai dai ya ce wannan karon sake ruwan bai zai kasance mai hadari sosai ba, domin damina ta ja, ruwan ya ragu, kuma wannan shi ne karo na karshe da za a saki ruwan daga Kamaru a bana.

Hukumomi dai sun bayyana cewa mutane kimanin dubu dari daya ambaliyar ta raba da muhallansu a jihar ta Benue, amma dai kamar dubu ashirin da biyar ne ke zaune a sansanoni; wadanda ba sa sansanoni kuma sun je gidajen 'yan uwa da abokan arziki.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.