BBC navigation

Takaddama tsakanin Syria da Turkiyya

An sabunta: 4 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:13 GMT

Wajen da aka kai wa hari da ke kan iyakar Syria da Turkiyya

Gwamnatin kasar Turkiyya ta mayar da martani cikin fushi game da kisan da wata tankar yaki da aka cilla daga Syria ta yi wa 'yan kasarta guda biyar.

Tankar yakin ta rushe wani gida a garin Akcakale da ke kan iyakar kasashen biyu.

Cikin wadanda suka rasu har da wata mata, da 'yayanta su uku, kana wadansu mutane kimanin goma suka samu raunuka.

Wadansu majiyoyi sun ce Turkiyya ta harba wadansu makamai a kan sojin Syria da ke aiki a garin Idlib.

Ministan watsa labarai na Syria, Omran Zoabi, ya ce suna gudanar da bincike don gano daga inda aka kai harin:

''Hukumomi na gudanar da bincike don gano daga inda aka kai wannan hari, wanda ya yi sanadiyar mutuwar wata mata, da 'yayanta a kan iyakar Syria da Turkiyya.Muna mika ta'aziyarmu ga iyalan wadannan mutane da suka yi shahada, da kuma al'umar Turkiyya, wadanda 'yan uwanmu ne, kuma abokai''.

Ana sa rai cewa ranar Alhamis Majalisar Dokokin Turkiyya za ta gudanar da wani zama na musamman inda gwamnatin kasar za ta bukaci amincewarta don fuskantar Syria.

Wannan lamari na faruwa ne bayan da wadansu jerin hare-haren da aka kai da bama-bamai suka yi kaca-kaca da wani dandali na gwamnati da ke tsakiyar birnin Aleppo na arewacin kasar, inda aka kashe fiye da mutane talatin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.