BBC navigation

Najeriya: An daure ma'aikatan hukumar yaki da cin hanci

An sabunta: 5 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:07 GMT

Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Lamurde

Wata kotu a Najeriya ta yanke hukuncin daurin shekaru biyar kan wasu tsofaffin ma'aikatan hukumar yaki da cin hanci da rashawa a kasar saboda zarginsu da neman na-goro daga wajen wani dan siyasa.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati wato EFCC ta ce ma'aikatan nata guda biyu sun bukaci dan siyasar, mai suna Kullima Kachalla, ya ba su cin hancin naira dubu dari, su kuma su lalata wasu takardun shaida a kan zargin da ake yi masa na almundahana da dukiyar kasa.

Hukumar ta ce Mista Kachalla ya sanar da ita game da wannan yunkuri na karbar cin hanci da ma'aikatanta suka yi, inda aka kama su ta hanyar yi musu gadar-zare.

Najeriya dai ta yi fice wajen cin hanci da rashawa lamarin da masu sharhi ke cewa shi ya yi sanadiyar fuskantar koma-bayan da take yi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.