BBC navigation

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da Syria

An sabunta: 5 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:11 GMT

Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon

Kwamatin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi tir da Syria saboda harin da tankar yakinta ta kai wa wani gari da ke Turkiyya lamarin da ya yi sanadiyar rasuwar Turkawa biyar cikinsu har da mace da yara.

Wata sanarwar da Kwamatin ya fitar, ta ce irin wannan hari yana barazana ga kasashe makwabtan Syria.

Sanarwar, wacce jakadan kasar Guatemala na din-din-din a Majalisar, wanda shi ne shugaban Kwamatin Sulhu, Gert Rosenthal, ya gabatar ta ce mambobin Majalisar sun yi matukar kaduwa da jin labarin kai harin.

Ya kara da cewa dole ne Syria ta kaucewa faruwar irin wadannan hare-hare a nan gaba.

Mista Rosenthal ya ce: ''Mambobin Kwamatin Sulhu na mika ta'aziyarsu ga iyalan wadanda wannan lamari ya shafa, da gwamnati da ma al'umar Turkiyya.

A nasa bangaren, Firayim Ministan Turkiyya, Recep Tayep Erdogan, ya ce duk da yake harin da Syia ta kai wa kasarsa ya bakanta musu rai, amma kasar ba ta da niyyar gwabza yaki da Syria.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.