BBC navigation

Sao Paulo: Birni mai cunkoson motoci

An sabunta: 5 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 18:00 GMT
Cunkoson ababen hawa a Sao Paulo

Cunkoson ababen hawa a Sao Paulo kan kai kilomita 180

Ina masu korafin sun makale a cunkoson ababen hawa (ko "go-slow", kamar yadda aka fi saninsa a Najeriya)? Nan gaba kafin ku yi korafin, ku tuna da masu ababen hawa a birni mafi girma a Brazil, daya daga cikin wuraren da ake samun cunkoso mafi muni a duniya.

Da zarar an ce yamma ta yi, musamman ranar Juma'a, sai hankalin masu ababen hawa a Sao Paulo ya tashi.

A lokacin ne cunkoson ababen hawa masu shiga da masu fita daga birnin kan kai jumlar kilomita dari da tamanin a cewar masana harkar tafiyar da ababen hawa; ya kan kuma kai kilomita dari biyu da casa'in da biyar a ranakun da ya kazance.

Danjojin ababen hawa kawai za a rika hange har iya inda idon mutum zai iya hangowa—suna kamawa suna daukewa yayin da direbobi ke taka burki suna daga kafa, har tsawon sa'o'i da dama.

'Kai ka ce teku ce'

Fabiana Crespo

Fabiana Crespo ta hadu da mijinta ne a cunkoson ababen hawa

"Kai ka ce teku ce. Tekun motoci", inji Fabiana Crespo, yayin da take kutsa kai cikin cunkoson tare da jaririnta dan wata goma, Rodrigo.

"Da ina zaune ne da dangina a kudancin Sao Paulo, yayin da nake aiki a karshen gari ta daya gefen.

"Saboda haka da na yi aure sai na yanke shawarar komawa arewacin birnin kusa da inda nake aiki, saboda zirga-zirgar ba dadi", inji ta.

"Amma bayan haihuwa ta ta farko sai na yanke shawarar ci gaba da kula da harkar kasuwancin dangina a tsohuwar unguwar da nake. Shi ya sa na sake fadawa cikin wannan kalubale na ketawa ta tsakiyar birnin idan zan je aiki".

Wannan tafiya dai kan dauki Crespo fiye da sa'o'i biyu a tafiya, sa'o'i biyu a dawowa—kuma kullum.

Matsala

Cunkoson ababen hawa kan haifar da matsala a ko ina a fadin duniya, ba kawai ga direbobi ba, amma a Sao Paulo ya zama karfen kafa.

Cunkoson ababen hawa ya zama rayuwa da al'adar mutanen wannan katafaren birni mai kunshe da al'umma fiye da miliyan goma sha daya.

"Mun zama bayin go-slow; don haka gaba daya rayuwarmu muna tsara ta ta dace da shi"

Fabiana Crespo

"Mun zama bayin go-slow; don haka gaba daya rayuwarmu muna tsarata ta dace da shi", inji Crespo.

Ya zuwa lokacin da za ta isa gida bayan kwashe wadansu karin sa'o'i biyu, almuru ya riga ya yi, mijinta da dansu dan shekara uku, Pedro, sun zaku su ga dawowarta.

Sai dai kuma a wani abu mai kama da almara, ta kan tuna cewa a irin wannan cunkoso ne shekaru tara da suka gabata ta hadu da mutumin da ta aura daga bisani.

"Ina tare da wata kawata a motata, shi ma yana tare da abokinsa a motarsa. A go-slow muka fara tafiya kafada-da-kafada, sai ya fara kallo na", inji Crespo.

Bayan an dan yi barkwanci ta tagogin mota, daga karshe Mauricio ya shawo kan Fabiana ta ba shi lambar wayarta. Bayan ya kirata, sai aka tsunduma cikin kogin soyayya.

A cewarta, "Ina ganin wannan ne kawai abin da ba ma korafi a kansa dangane da cunkoson ababen hawa a Sao Paulo".

Babban titin Marginal Pinheiros titin ne mai muhimmanci a Sao Paulo

Sai dai masu ababen hawa da yawa labarin da za su bayar na takaici ne; har ma gidajen radiyo kan ware lokaci musamman don tabbatar da cewa masu ababen hawan sun samu cikakkun bayanai.

Daya daga cikin gidajen radiyon ma ba shi da aiki sai bayar da rahotannin yanayin cunkoso da wadansu hanyoyin masu saukin cunkoso—aikinsa ke nan dare da rana, safe da yamma.

Tun bayan kafa shi shekaru bakwai da suka gabata, gidan radiyon mai suna "Sul America Traffic Radio" ya tara masu sauraro da dimbin yawa wadanda kuma su ne masu aiko masa da rahotanni ta hanyar bugo waya su sanar da sauran masu ababen hawa halin da hanya ke ciki ko kuma su fadi irin takaicin da suke ciki.

A lokutan da ake samun cunkoso, tashar kan yi amfani da jirgin sama mai saukar ungulu, da kuma gungun masu aiko da rahotanni wadanda su ma ke makale a cikin cunkoson.

Daya daga cikinsu ita ce Victoria Ribeiro, wacce aka baiwa aikin zagayawa don gano wuraren da cunkoso ya yi yawa da kuma hanyoyin kauce masa.

"Tun da aka kafa tashar radiyon nake aiki da ita kuma muna ganin abin kara kazancewa ya ke yi yayin da motocin da ke hawa kan tituna ke karuwa", inji Ribeiro.

A shekaru goman da suka gabata dai masana'antun kera motoci a Brazil suna ta tserereniya wajen kera motoci yayin da miliyoyin al'umma ke kara wadata saboda habakar da tattalin arzikin kasar ke yi.

Mallakar mota babban buri ne ga jama'a da dama, saboda tana bayar da damar kaucewa motocin haya wadanda ba su cika inganci ba, sannan kuma alama ce ta wadata.

Sai dai kuma, ko da yake yawan sayen motoci na da muhimmanci wajen tallafawa ci gaban tattalin arzikin Brazil, a lokaci guda kuma ya kai ambaliyar "tekun motoci" a Sao Paulo wata sabuwar makura.

'Abin ya yi kama da yaki'

"Abin tamkar yaki ne, saboda duk wanda ya ya tsinci kansa rike da sitiyarin mota, to kansa kawai ya sani", inji Ribeiro.

Wadanda ke da wadata sosai dai na da wani zabin—a zahiri za su iya bi ta kan wannan matsala a 'tasin sama'.

Saboda kazancewar cunkoson ababen hawa da kuma tsoron fashi—abubuwa biyu da suka addabi mutanen Sao Paulo—wadanda ke daukar masu hannu-da-shuni da ma jami'an manyan kamfanoni suna kai su sassan birnin daban-daban da jirage masu saukar ungulu kasuwar su ta bude.

Masu hannu da shuni a jirage masu saukar ungulu suke yawo

"Idan na dauki hayar jirgi mai saukar ungulu na 'yan sa'o'i kadan, zan iya tashi daga wuri zuwa wuri in halarci tarurruka uku ko hudu a yini guda—abin da ba zai yiwu ba idan a mota zan rika yawo", inji Sergio Alcibiades, wani mai bayar da shawara ta fuskar shari'a wanda kan dauki hayar tasin sama. "A ganina wannan wata hanya ce ta samun kudi".

Mutumin da ya mallaki kamfanin tasin sama mai suna Helimart Air Taxi, Jorge Bittar, ya ce kamfaninsa ba bunkasa da kashi goma cikin dari duk shekara, kuma yana da jirage masu saukar ungulu har goma sha shida wadanda ba sa jimawa a kasa.

"In dai batun cunkoson ababen hawa ne, to mu ya ma kara kazancewa don kuwa, a dadin ma-sha kara, wai dawa ta ki fidda kai", inji Mista Bittar.

Ko da yake cunkoson ababen hawa ya bude kofar samu ga wadansu mutane, yana kuma yin mummunan tasiri a kan tattalin arzikin kasa.

'Cunkoso na haddasa tsadar kayayyaki'

Mummunan cunkoson ababen hawa kan haddasa tsadar rayuwa da kuma tsadar gudanar da harkokin kasuwanci, a cewar Claudio Barbieri, wani kwararren malami a kan aikin injiniya da sufuri a Jami'ar Sao Paulo.

"Idan kana da babbar mota, kuma ya kasance wannan mota taka ba za ta dauki kaya fiye da sau shida ko takwas ba a maimakon sau goma sha biyar ko ashirin, to kana bukatar manyan motoci guda biyu. Saboda haka komai sai ya kara tsada".

Farfesa Barbieri ya kuma ce Sao Paulo na da kwararrun injiyoyi masu kula da zirga-zirgar ababen hawa wadanda kan taimaka komai ya tafi yadda ya kamata sai dai sannu ba ta hana zuwa.

"Babu wani birni a duniya da zai iya kawo karshen cunkoson ababen hawa, saboda idan ababen hawa na tafiya mutane za su yi ta shiga mota"

Claudio Barbieri

"Matsalar ita ce mu mutanen Brazil ba mu iya kyakkyawan tsari ba; cunkoso zai fara raguwa ne kawai idan muka fara nemo maslaha ta dogon lokaci", inji Farfesa Barbieri.

Ya kuma kara da cewa, "Babu wani birni a duniya da zai iya kawo karshen cunkoson ababen hawa, saboda idan ababen hawa na tafiya mutane za su yi ta shiga mota. Muhimmin al'amari shi ne a samu daidaito, inda mutane za su yi amfani da ababen hawa na gwamnati saboda sun fi sauri.

"Saboda haka Sao Paulo na bukatar zuba jari cikin gaggawa a harkar sufuri ta gwamnati a maimakon gina sababbin hanyoyin mota wadanda za a kara cika su da motoci".

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.