BBC navigation

'Yan sanda sun kaddamar da farmakin yaki da ta'addanci a Faransa

An sabunta: 6 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:13 GMT
Farmakin 'yan sandan Faransa

Kasar Faransa na yaki da musulmi masu tsatsauran ra'ayi

'Yan sandan Faransa sun harbi wani mutum tare da yi masa mummunan rauni a lokacin wani farmakin yaki da ta'addanci da su ka kaddamar a birnin Strasbourg

An kuma kai farmakin a wasu birane da su ka hada da Paris, a wani bangare na kama gungun wadanda ake zargin masu tsautsauran ra'ayin addinin Islama ne

An kuma tsare mutane bakwai

Wakilin BBC a Paris yace binciken ya maida hankali ne akan wani harim bam da aka kai kan wani dakin ajjiye kaya na yahudawa a birnin Paris makonni uku da suka gabata

Shugaban Kasar ya jaddada cewar a shirye gwamnatin sa take ta kare 'yan kasar daga dukkanin wata barazanar ta'addanci

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.