BBC navigation

Mutane sun mutu a hatsarin jirgin sojin Kasar Sudan

An sabunta: 7 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:18 GMT
Hatsarin Jirgin sojin Sudan

Jirgin sojin Sudan ya rabe gida biyu

Wani jirgin sojin Kasar Sudan dauke da mutane fiye da 20 ya yi hatsari a wajen babban birnin Kasar na Khartoum.

Gidan talabijin din Kasar yace mafi yawa daga cikin wadanda ke cikin jirgin sun mutu.

Jirgin dai ya rabe gida biyu, a lokacin da yake yunkurin saukar gaggawa, bayan da matukin jirgin ya bada rahotan wasu matsaloli a cikin injin jirgin

Jirgin dai yana tafiya ne daga Khartoum zuwa Darfur, a lokacin da yai hatsarin.

Ko a watan Agusta ma dai, mutane fiye da 30 ne suka mutu a wani hatsarin jirgi a kudancin Kasar, wanda ya hada da 'yan siyasa da kuma manya janar- janar na soji

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.