BBC navigation

An soma zaben Shugaban Kasa a Venezuela

An sabunta: 7 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:05 GMT
Zaben Venezuela

Shugaba Hugo Chavez zai kara da Henrique Capriles

Jama'a a Venezuela na kada kuri'arsu a zaben Shugaban Kasar mafi zafi, tun lokacin da Shugaba Hugo Chavez ya dare kujerar mulki

Shugaban dai yana neman wa'adi ne na nuku, sai dai babban abokin hamayyar sa Henrique Capriles, na samun goyan bayan jam'iyyun adawa 30 a Kasar

Mr. Capriles ya yi alkawarin ci gaba da wasu shirye shirye na jin dadin jama'a, amma ya yi watsi da irin salon mulkin Shugaba Chavez

Ana dai tsammanin samun sakamakon zabe da sanyin safiyar ranar litinin

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.