BBC navigation

Venezuela na zaben Shugaban kasa

An sabunta: 7 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 06:57 GMT

Zaben kasar Venezuela


A safiyar yau Lahadi ne 'yan kasar Venezuela za su fara kada kuri'unsu a zaben da ake hasashen za a yi hamayya ta kut-da-kut; tun bayan da Hugo Chaves ya kama ragamar mulkin kasar.

Mr Chaves wanda aka fara zaba tun a shekarar 1998, yana neman wani wa'adin mulki ne karo na hudu don cigaba da abinda ya kira juyin-juya hali na 'yan gurguzu a kasar mai arzikin man fetur.

Sai dai kuma yana fuskantar babban kalubale daga Henrique Capriles wanda jam'iyyun adawa talatin ke rufa masa baya, wanda kuma ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar.

Kimanin sojoji dubu dari ne aka tura rumfunan zaben, ana kuma sa ran samun sakamako da sanyin safiyar litinin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.