BBC navigation

FARC ta ce 'yansanda sun janye kama magoya bayanta

An sabunta: 8 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 04:51 GMT

Dakarun Cambodia

Babbar Kungiyar tawaye ta masu ra'ayin kawo sauyi watau FARC ta ce hukumar 'yansandan duniya ta janye sammacin kame magoya bayan ta da za su shiga shawarwarin da za a yi na sulhu da gwamnatin Colombia.

Wani babban jam'i'i a Kungiyar ta FARC Rodrigo Granda ya yi marhabin da wannan mataki yana cewa wannan ya nuna gwamnatin Colombia tana mutunta alkawurran da ta dauka na yarjejeniyar neman zaman lafiya.

Bangarorin biyu suna gab da kulla wata yarjejeniya mai dimbin tarihi ta kawo karshen rikicin da aka shafe kimanin shekaru hamsin ana yi a tsakaninsu.

Bukatar janye wannan sammaci yana daya daga cikin bukatun kungiyar 'yan tawayen da suka gabatar gabanin shawarwarin sulhun da aka shirya farawa nan gaba cikin wannan watan a kasar Norway.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.