BBC navigation

Harin bam ya raunata sojoji a Maiduguri

An sabunta: 8 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 13:27 GMT
Shugaban 'yan sandan Najeriya, Muhammed Abubakar

Shugaban 'yan sandan Najeriya, Muhammed Dahiru Abubakar

Rundunar tsaro ta hadin gwiwa, JTF a Maiduguri ta ce an kai mata harin bam da safiyar yau, inda aka raunata sojoji biyu dake cikin wata mota akori kura kirar Hilux.

Sai dai mazauna birnin sun yi zargin cewa, harin da aka kai a Lagos street ya sa sojojin shiga gida-gida, inda suka kashe fararen hula takwas.

Kakakin rundunar JTF, laftanar Kanar Sagir ya ce kawo yanzu ba su kama kowa a kan harin ba, kuma babu wanda ya fito ya dauki nauyin kai harin.

Harin 'ya zo ne kwana daya bayan wasu 'yan bindigan da ba a san ko su wanene be, sun harbe wani dan kasar Sin a kasuwar Gubio dake birnin.

Dan kasar China na aiki da wani kamfanin gyaran hanyoyi a birnin na Maiduguri, kuma ya je kasuwar ne domin sayen rago lokacin da 'yan bindigan suka harbe shi.

Jihar ta Borno dai ta dade tana fuskantar hare-haren bama-bamai, wanda a wasu lokutan kungiyar nan ta jama'atu Ahlu sunna lidda'awati wal jihad da akafi sani da Boko Haram kan dauki nauyin kai su.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.