BBC navigation

Mitt Romney ya soki manufofin Obama

An sabunta: 8 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:38 GMT

Dan takarar jam'iyyar Republican a zaben da za a yi a Amurka, Mitt Romney, ya yi kakkausar suka ga manufar harkokin wajen Shugaba Obama.

Mr Romney yayi ikirarin cewa hadarin fadawa cikin rikici a yankin Gabas Ta Tsakiya yana da girma yanzu, fiye da a lokacin da Mr Obaman ya hau kan karagar mulki.

A wani jawabi da ya yi a Virginia, Mr Romney ya zargi shugaba Obama da jagorantar kasar ta bayan fage tare da jefa Amurka cikin hadari.

Ya ce: "Ba za mu iya marawa kawayenmu baya tare da murkushe abokan gabanmu a Gabas Ta Tsakiya ba, idan ba ma cika alkawarukan da muka yi, idan kuma muna rage kudaden da muke kashewa a fannin tsaro".

Mr Romney ya ce hare-haren da aka kaiwa ofisoshin jakadancin Amurka a kwanan baya ba irin na kan mai tsautsayi ba ne, inda ya dora alhakinsu a kan kungiyar al-Qaida.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.