BBC navigation

Amnesty ta yi kira ga Rwanda ta binciki zargin azabtarwa

An sabunta: 8 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 06:26 GMT

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Rwanda ta binciki zargin sojojin kasar da ake yi cewa suna kame mutane siddan-ragadan tare da gana musu azaba.

Kungiyar Amnesty ta ce a tsakanin watan Maris na shekara ta 2010 zuwa watan Yunin wannan shekarar ta samu bayanai na mutane arba'in da biyar da aka kama ba gaira ba dalili kuma aka gana musu azaba.

Kungiyar ta ce, ta fahimci gwamnatin Rwandar tana kokarin kawo karshen cin zarafin mutane da ake yi, to amma gwamnatin Rwandar ma ta musanta cewar ana kame mutane siddan ragadan ana tsare su.

Ana zargin dai an yi amfani da duka da kuma jan wutar lantarki don tilastawa a amsa laifi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.