BBC navigation

Girkawa ba su yi marhabin da zuwan Ms Merkel ba

An sabunta: 9 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:20 GMT
Masu zanga zanga a Athens

Masu zanga zanga a Athens

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel wacce ke ziyara a Athens, ta fadawa Girkawa cewar suna samun nasara wajen magance matsalolin tattalin arzikin kasar, amma tace akwai jan aiki a gaba.

Dubun dubatar mutane dake zanga zanga akan matakan tsuke bakin aljihu dai, sun hallara kusa da majalisar dokokin Kasar Girkan.

'Yan sandan kwantar da tarzoma sunyi amfani da hayaki mai sa hawaye domin maida masu zanga zangar baya.

Girkawa da dama dai na cike da fushi da kasar Jamus, ganin cewar ita ke jagorantar kiraye kirayen zaftare albashi da kuma tallafin da aka basu da kaso mai tsoka, saboda a samu damar ceto tattalin arzikin Kasar da yake kan hanyar dukurkushewa.

Ga abinda daya daga cikin masu zanga zangar yake cewa

CLIP one

Muna son isar da babban sako akan cewar bamaa kin al'ummar Jamus, amma kuma manufofin da aka kirkiro a tsakanin kasashen Turai da Jamus ke jagoranta sune abun kii.

Shi kuma wannan cewa yayi

CLIP two

A irin wannan lokacin kasarmu bata da makoma me kyau. Sun dakushe makomar matasa. Abinda suke yi mana albishir shine kawai zamu ci gaba da zanga zanga akan tituna har na tsawon shekaru talatin masu zuwa. Sun kashe mana rayuwa.

Wannan ne ziyara ta farko da Misis Merkel ta kai kasar Girka tun lokacin da tattalin arzikin kasashen Turai ya soma fuskantar matsaloli kusan shekaru uku da suka wuce. Galibin al'ummar Girka na jin haishin Jamus ne saboda itace ta ce a rage yawan albashi da kuma irin tallafin da gwamnati ke baiwa al'ummarta, don kungiyar tarayyar turai ta baiwa Girkar kudaden ceto tattalin arzikinta.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.