BBC navigation

IMF:An ci baya kan farfado da tattalin arziki

An sabunta: 9 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:19 GMT

Shugabar IMF Christine Lagarde

Hukumar ba da lamuni ta duniya IMF ta ce an samu ci-baya a yunkurin da ake yi na farfado da tattalin arzikin kasashen duniya.

A yanzu dai hukumar ta IMF ta sassauta hasashen da ta yi na habakar tattalin arzikin duniya zuwa kashi uku bisa dari a wannan shekarar da badi.

A wani sabon rahoto da ta bayar, hukumar ba da lamunin ta duniya ta ce babbar matsalar ita ce manufofi na tattalin arziki a kasashen da suka cigaba sun gaza karfafa wa jama'a gwiwa.

Wani babban masanin tattalin arziki a hukumar ta IMF Olivier Blanc-hard ya ce babban abin damuwa shi ne yiwuwar farfadowar tattalin arzikin kasashen Turai da halin da harkokin tattalin arziki na gwamnatin Amurka suke ciki.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.