BBC navigation

"Sojoji sun hallaka fararen hula a Najeriya"

An sabunta: 9 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:18 GMT

Jamian tsaro a Maiduguri

Rahotanni daga Arewa maso gabashin Najeriya na cewa Sojoji sun hallaka fararan hula akalla talatin bayan da aka sawa motar sintirin Jamian tsaro na hadin gwiwa wato JTF bam, harin ya raunata jamian biyu.

Rahotannin dai na cewa wannan dalilin ne yasa Sojojin suka budewa mutane wuta a yankin tare da cinnawa wasu shaguna da gidaje wuta.

Harbin kan mai uwa da wabi da ake zargin Rundunar tsaron ta hadin gwiwa JTF wadda take da alhakin kare rayukan mutane da dukiyoyi ya dimauta jama'a da dama.

Da ma dai akan yi zarge-zarge a baya cewa Rundunar tsaron na musgunawa jama'a gami da kashe wadanda basu ji ba basu gani ba.

Rahotanni daga Asibitin Umaru Shehu dake birnin Maiduguri na nuni cewa an kai gawawwakin mutane sama da talatin farar hula wadanda galibin su na da raunin harbin harsashi.

Haka kuma wani dan Jarida a birnin ya shaidawa BBC cewa ya ga gawawwaki kusan talatin.

Tun bayan da Kungiyar Ahlusunna Lilda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko haram suka fara kai hare haren bama bamai da na bndigogi a arewacin kasar, mazauna Jihohin Borno da Yobe suke cikin halin gaba kura baya sayaki.

A baya dai an zargin Jamian tsaron da cinnawa wata kasuwa wuta a birnin gami da farma wasu mutane a gidajensu.

Sai dai Kakakin Rundunar JTF Sagir Musa ya musanta kashe fararan hular da ake zargin Jamian tsaron suna yi a Birnin.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch a 'yan kwanakin nan ta yi kira da a gurfanar da jami'an tsaron da ake zargin su da cin zarafin al umma a gaban kotu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.