BBC navigation

Najeriya ta barwa Kamaru yankin Bakassi

An sabunta: 9 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:34 GMT
Taswirar yankin Bakassi

Taswirar yankin Bakassi

Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta daukaka kara ba, game da batun tsibirin Bakassi mai albarkatun man fetur, bayan da kotun duniya dake Hague ta yanke cewa yankin mallakar kasar Kamaru ne.


Gwamnatin Najeriyar dai ta bada dalilan cewa yin hakan na iya yin mummunar illa ga zaman takewar kasashen biyu.


Tuni dai wannan mataki da gwamnatin tarayyar Najeriyar ta dauka na kin dauaka karar ya gamu da kakkausar suka
daga bangarori daban-daban a jihar Kuros Riba, wadda daga cikinta ne aka yanke tsibirin na Bakassi.


Har 'yan majalisar dokokin jihar sun yi wata zanga-zangar lumana a fadar gwamnatin jihar, suna neman a dau tsattsauran mataki kan ministan shari'a na kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.