BBC navigation

Hadewar BAE da EADS ta ci tura

An sabunta: 10 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:36 GMT
Hadewar kamfanonin BAE da EADS

Hadewar kamfanonin BAE da EADS

An yi watsi da wani shiri na hade Kamfanin kera makaman yaki na Burtaniya wato BAE Systems da kuma wani katafaren kamfanin harkokin sararin samaniya mallakar Faransa da Jamus wato EADS.

Yarjejeniyar wacce zata haifar da wata huldar kasuwancin samar da kayayyakin da ake amfani da su a sararin samaniya da kuma makaman kariya mafi girma a duniya, na bukatar amincewar gwamnatocin Burtaniya da Jamus

Kamfanonin sunce ta bayyana a fili cewa muradun wadannan Kasashe biyu sun sha bambam

Burtaniya dai na bukatar takwararta ta amince ta takaita karfin da take da shi a shirin kawancen, domin tabbatar da dangantaka tsakanin Kamfanin BAE tare da Gwamnatin Amurka ta cigaba da kasancewa mai karfi

An dai fahimci cewa gwamnatin Jamus tayi adawa da hakan

Idan da ace anyi nasarar hade wadannan kamfanonin, to da za a samu wani katafaren kamfanin harkokin tsaro da safarar jiragen sama na farar hula dana soji wanda ya zarce kamfanin Boeing na Amurka.


Kamfanin BAe Systems na Birtaniya da kamfanin EADS, mallakar Faransa da Jamus, mai kera jiragen sama na Airbus, sun so su hade ne don samar da babban kamfanin harkar tsaro da safarar jiragen sama mai karfi sosai a duniya.


To amma shirin nasu ya fada cikin matsalar rashin amincewar shugabannin siyasa a kasashen ukku.


Gwamnatocin Faransa da Jamus basu son su rage yawan hannun jarin da suke dashi a kamfaninsu.


Ita kuma Birtaniya ta damu ne da batun yiyuwar korar ma'aikatan kamfanin BAE a Birtaniyar da kuma kwanturagin harkokin soji a Amurka, idan har aka aka ga cewa gwamnatocin Turan na kokarin tsoma baki ne cikin lamarin.


Ita dai Birtaniyar ba ta so gwamnatocin kasashen su tsoma baki sosai, don kamfaninta na BAE ya cigaba da yin dangataka ta gari da Amurka. To amma Jamus ta nuna adawa ga hakan.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.