BBC navigation

Muamba ya damu kan matakin da aka dauka akan kocin Bolton

An sabunta: 10 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 13:26 GMT
player

Fabrice Muamba

Tsohon dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Bolton Wanderers Fabrice Muamba ya damu gameda da korar da aka yiwa Owen Coyle kuma ya ce ya kamata, wanda zai maye gurbinsa ya yi kokarin ganin kungiyar ta samu karin girma.

A ranar talata da ta gabata ne aka kori Coyle daga aiki sakamakon rashin taka rawar gani a wasannin da suka buga bayan kungiyar ta fado daga matakin da take.

A watan Augustan da ya gabata ne Muamba ya yi shellar zai yi retiya daga buga kwallon kafa bayan bugun zuciyar da ya samu a filin wasa a watan Maris din daya gabata.

" Na damu amma na san shugabannin kungiyar zasu kawo wani da zai sa kungiyar ta sami karin girma saboda muna bukatar karin gima".

"Ban ji dadin korar da aka yiwa Owen ba amma ya kamata ayi la'akari da wasu abubuwa".

Jama'a da dama sun yabawa kungiyar kwallon kafa ta Bolton da tsohon kocinta gameda da goyon bayan da suka nuna wa tsohon dan wasan Arsenal bayan zuciyarsa ta buga a karawar da suka yi da kungiyar Tottenham Hotspur a zagayen Qauter final a gasar FA a watan Maris din daya gabata.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.